Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya yi babban rashin aminin sa

Published

on

Bayan da Allah ya yi masa rasuwa a jiya Litinin  tsohon minista a jamhuriya ta biyu Malam Isma’ila Isa Funtuwa a Abuja yana da shekaru 78, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar a matsayin babbar rashi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar daya daga cikin abokansa, malam Isma’ila Isa Funtuwa.

Sai dai ba’a bayyana dalilinan rasuwar marigayi Malam Isma’ila Funtuwa ba, amma wata majiya ta ce, rasuwar ta sa ba zata rasa nasaba da bugun zuciya ba.

A cewar shugaba Buhari rasuwar Malam Ismaila Funtuwa ya bar babba gibi mai wuyar cikewa.

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.

Sanarwar ta ruwaito shugaba Buhari na taya ‘yan uwa da abokan arziki da kuma al’ummar jihar Katsina game da wannan babbar rashi da su ka yi.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!