Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari zai gina wa jami’an NDLEA bariki

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da gina bariki ga ma’aikatan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a fadin kasar nan.

Shugaban hukumar NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa Mai ritaya ne ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar gwamnati.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan yayi wata ganawa da shugaba Buhari a fadar sa, don yi masa bayanin ayyukan hukumar.

Shugaban na NDLEA ya ce gina barikin ga ma’aikatan hukumar ya zama wajibi ko don kare su da iyalansu daga masu aikata miyagun laifuka.

Buba Marwa ya buga misali da cewa, mafi yawa daga jami’an tsaro irin su Sojoji, yan sanda, Kwastam, hukumar kula da shige da fice, suna da bariki, amma ban da NDLEA.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!