Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya amince da daukan jami’an ‘yan sanda dubu 10 duk shekara-IG

Published

on

Gwamnatin tarayya ta amince da daukar jami’an ‘yan-sanda dubu 10 kowacce shekara, domin ‘kara yawan jami an, da kuma ingantuwar tsaro a fadin kasar.

Babban sefeton ‘yan-sandan kasar Usman Alkali Baba ne, ya bayyana haka, ya yin da ya ziyarci gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar a gidan gwamnatin jihar dake Dutse a jiya Juma’a 03 ga Satumbar shekarar 2021.

Usman Alkali ya ce, daga yanzu duk wani jami’I da rundunar ta dauka, za’a mayar dashi karamar hukumar da ya fito bayan an bashi horo.

Ya ce a bana, sabin jami’an ‘yan sanda dubu 20 za’ a dauka, sakamakon rashin samun damar daukar dubu goman shekarar bara ta 2020.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!