Labarai
Buhari ya ce an yi wa kudirin dokar ma’aikatar ruwa gurguwar fahimta
Gwamnatin tarayya ta yi karin gaske kan sake yin nazarin kudirin dokar da ta kafa ma’aikatar albarkacin ruwa ta shekara ta 2020, ta na mai cewa ‘yan Najeriya ba su fahimci inda dokar ta sanya gaba ba,
Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya sanar da hakan a taron manema labarai a Abuja tare da ministan albarkantun ruwa Suleman Adamu gwamnatin tarayya zata tabbatar da an zartar da kudirin dokar saboda cigaban ‘yan Najeriya.
Alhaji Lai Muhammed ya kara da cewar, da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun yi wa kudirin dokar gurguwar fahimta kasancewar bas u karanta kudirin baki day aba.
Adai kwanakin baya ne wasu ‘yan Najeriya da kungiyoyi ksihin al’umma suka yi ta caccakar kudirin dokar ma’aikatar ruwan bayan da wasu mutane suka caccaki sun ki amincewa da sabuwar dokar ga kafafan yada labarai.
You must be logged in to post a comment Login