Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zargin fyade : Kotu ta wanke wani matashi a Kano

Published

on

Babbar kotun jiha wacce  mai shari’a Dije Abdu Aboki ke jagoran ta, ta wanke wani matashi mai suna Saifullahi Haruna Kabo da ake zargin da aikata fyade ya yin da ta sallami shi.

A dai kwanakin baya ne ake zargin matashin Saifullahi Haruna Kabo da laifin hada baki da kuma laifin fyade, bayan kuma kotun ta gano ba shi da laifi.

Sai dai kafin wanke shi Saifullahi Haruna Kaboa ya kwashe  tsawon shekaru uku a gidan gyaran hali.

Bayan da mai shari’a Dije Abdu Aboki ta wanke shi da safiyar yau  wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il  ya zanta da matashin  yana mai  bayyana jin dadin sa akan yadda kotun ta gane bashi da laifi kan zargin yi wa wata yarinya fyade.

Kotu a Kano ta aike da Kansila gidan gyaran hali

Kotu ta yi sammacin shugaban KAROTA

“Ya na mai cewa, kotu tayi min adalci ta duba tayi bincike ta gane mai laifi, kuma da ba ni da laifi ta sake, nayi matukar godiya
Ya kuma ce, shekaru ukun da nayi a gidan gyaran hali, na koyi darussa da dama, dole ka tsaya ka gina rayuwar ka, idan kana yin abun da ba daidai ba ne ka gyara, kuma kurkuku gida ne na gyaran hali, idan ka so ka gyara”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!