Connect with us

Labaran Kano

Buhari ya ce a gobe Talata za’a kaddamar da shirin daukar ma’aikata

Published

on

A  gobe talata ne gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da shirin daukar ma’aikatan wucin gadi dubu dari 7 da 74 a fadin kasar.

Karo na 3 kenan ana dakatar da shirin.

A shafinsa na tuwita karamin Ministan Kwadago da samar da ayyuka na kasar Festus Keyamo,ya ce an kammala dukkan shirye-shirye na kaddamar da daukar ma’aikatan, kuma za’a dauki mutum dubu 1 a kowacce karamar hukuma dake kasar nan.

Za’a biya naira dubu 20 a matsayin alawus ga ma’aikatan wucin gadin a kowanne wata,  tsawon watanni 3 da za’ayi ana shirin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!