Connect with us

Labarai

Mun kammala rarraba kayayyakin da basa bukatar tsaro – KANSIEC

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC, ta ce ta kammala rarraba kayayyakin da basa bukatar tsaro na zaben kananan hukumomin da za a gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Janairun da muke ciki a kanana hukumomin 44 na jihar.

Shugaban hukumar Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bayyana hakan, jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi nan tashar Freedom rediyo da ya mayar da hankali shirye-shiryen da hukumar ke yi na gabatowar zaben shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu.

Garba Sheka ya ce, tuni hukumar ta aike da kayayyakin da basa bukatar tsaro zuwa cibiyoyin zaben da ke kowacce karamar hukumar yayin da sauran kayayyakin za a kammala rabasu a ranar Laraba da Juma’ar jajiberan zaben.

Garba Ibrahim Sheka kenan, shugaban hukumar zaben kananan hukumomin KANSIEC cikin shirin Barka da Hantsi na yau, sai a biyo mu don jin cikakken rahoto kan yadda shirin ya kasance a labaranmu na gaba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!