Connect with us

Labaran Kano

Najeriya ba za ta taba durkushewa ba – Lai Muhammad

Published

on

Ministan Yada labaru Najeriya Alhaji Lai Muhammad ya ce kasar nan ba za ta taba durkushewa ba  har’abada, duk kuwa da mummunar fatan da’ake mata ko ta ko ina.

A watan Disambar bara jaridar Financial times ta Birtaniya ta wallafa cewa Najeriya na kan gabar wargajewa saboda yawan garkuwar da ake yi da jama’a da kuma ta’asar da barayin daji ke yi a kasar.

Sai dai a wani taron manema Labaru Ministan ya yi tur da wannan labari, yana mai cewa gwamnati na samun nasara a yakin da ta ke yi da masu aikta miyagun laifuka.

“Ya ce ba tun yanzu ba ake hasashen wargajewar kasarnan, amma hakan bai yuwuba kuma bazai taba yuwu din ba sam-sam”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!