Labarai
Buhari ya fara shirin jinginar da titin Kano zuwa Katsina da wasu 11
Gwamnatin tarayya a jiya talata ta fara shirye-shiryen jinginar da wasu manyan titunan tarayya guda goma sha biyu a sassa daban-daban na kasar nan.
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Rashola ya bayyana haka lokacin da yak e kaddamar da wani shafin internet ga wadanda ke bukatar a dama dasu cikin harkar jinginar da titunan.
Titunan guda goma sha biyu da gwamnatin tarayya ta ware wadanda za a jinginar da su suna da nisan kilomita dubu daya da dari tara da sittin da uku, wanda bai wuce kaso biyar da digoshida ba kacal cikin manyan titunan tarayya da nisansu suka kai kilomita dubu talatin da biyar.
Titunan da aka ware don jinginar da su sun hada da: Benin zuwa Asaba, Abuja zuwa Lokoja, Kano zuwa Katsina, Onitsha zuwa Owerri, Shagamu zuwa Benin da kuma Abuja zuw Keffi har ya kai ga Akwanga.
Sauran sune: Kano zuwa Shuwari, Potiskum zuwa Damaturu, Lokoja zuwa Benin, Enugu zuwa Fatakwal, Ilorin zuwa Jebba, Lagos zuwa Ota zuwa Abeokuta da kuma Lagos zuwa Badagry zuwa Seme.
You must be logged in to post a comment Login