Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya gargadi ‘yan Najeriya da su guji yiwa kan su gwajin Corona

Published

on

Gwamnatin tarayya ta shawarci al’ummar kasar nan da su guji yiwa kan su gwaji ko shan maganin Corona, ba tare da shawarar likitoci ba wanda hakan kan iya jawo musu ciwon Koda.

Babban Daraktan gudanar da Asibitocin gwamnatin tarayya, Dr Adebimpe Adebiyi, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi da kamfanin dillacin labarai na kasa a birnin tarayya Abuja.

Adebimpe, ya kara dacewa labarai da suka karade kasar nan musamman ta kafafen sada zumunta na Zamani na nuni da cewar amfani da Citta da Ruwan zafi da gishiri, tare da shan ruwa mai yawa na maganin cutar ta Corona.

Jami’in yace rade radin zai jawo koma baya tare da haifar da matsaloli da dama ga lafiyar al’umma da yayi kiran jama’a da su guji yin hakan tare da neman shawarwarin kwararru a harkar lafiya da zarar sunji sauyi a jikin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!