Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu : Mutumin da ya bata sunan Badaru zai zauna a gidan gyaran hali

Published

on

Wata kotun majistrate da ke zaman ta a Dutsen jihar Jigawa ta yankewa wani mutum mai suna Sabi’u Chamo hukuncin zama a gidan gyaran hali na tsahon watanni 6.

Kotun dai ta yankewa mutumin hukunci ne tare da cin tarar sa naira dubu 20 da kuma hukuncin bulala 20 sakamakon kama shi da laifin bata sunan Gwamnan jihar Muhammadu Badaru Abubakar.

Da ta ke yanke hukunci alkalin kotun mai shari’a Batula Dauda ta ce kotun ta kama mutumin da laifin bata sunan gwamna Badaru ta cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin sa na Facebook.

Rahotanni sun bayyana cewa da fari wanda ake zargin ya musanta laifin da ya aikata.

Sai dai kuma daga bisani kotun ta kama shi da laifi bisa kwarararan hujjojin da masu kara suka gabatar mata, inda ta yanke masa wannan hukunci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!