Connect with us

Labarai

Buhari ya dawo daga ƙasar Saudiyya

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dawo gida daga ziyarar kwanaki biyar da ya kai ƙasar Saudiyya.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Buhari ya taso daga filin jirgin saman sarki Abdulaziz da misalin ƙarfe 3:45 inda ya sauka a Abuja da da ƙarfe 6 na yammacin ranar Juma’a .

Yayin da yake ƙasar Saudiyya shugaban ya halarci taron tatalin arziƙi karo na 5 da aka gudanar a birnin Riyadh na ƙasar.

Kazalika ya gabatar da ibadar Umrah a birnin Madina, har ma ya gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

Gabanin dawowar ta sa sai da ya gudanar da wata ganawa ta musamman da ƴan Najeriya mazauna ƙasar ta Saudiyya

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!