Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar jihar Zamfara

Published

on

Gwamnatin tarayya ta haramta duk wani aikin hakar ma’adanai a Jihar Zamfara tare da haramta shawagin jirage a sarararin samaniyar Jihar.

Mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya ne ya tabbatar da hakan yau ga manema labaran fadar shugaban kasa, bayan kammala taron majalisar koli kan harkokin tsaro ta kasa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci zaman majalisar na yau, a fadarsa da ke Abuja.

Ta cikin sanarwar, shugaba Buhari ya umarci ma’aikatar tsaro da mashawarcinsa kan harkokin tsaro da aike da sojoji tare da ingantattun kayan aiki domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.

Haka zalika shugaba Buhari ya kara da cewa tuni jami’an tsaron sirri na kasar nan suka fara sanya ido tare da bibiyar wandada ake zargi da tayar da tarzoma domin kakkabe su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!