Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Yahya Koshak, Mutumin da ya fara Yashe Rijiyar Zamzam Ya Rasu

Published

on

Dr. Yahya Koshak mutumin da ya fara shiga rijiyar Zamzam yayin wani aikin yasa da aka gudanar a alif da dari tara da saba’in da tara (1979), ya rasu yana da shekaru 80.

Dr Yahya Koshak ya rasu ne a jiya litinin daya ga watan Maris.

Ya kasance tsohon darakta janar na hukumar kula da albarkatun ruwa ta kasar Saudiya.

A cikin wata sanarwa da kwamitin ‘Haramain’ da ke kula da masallatan harami biyu da ke biranen Makkah da Madina ta fitar, ta ce, Injiniya Yahya Koshak shine mutum na farko da ya fara shiga cikin rijiyar Zamzam wanda aka sani a tarihi yayin wani aikin kwaskwarima da aka yiwa rijiyar a alif da dari tara da saba’in da tara (1979) lokacin mulkin Sarki Khalid.

Sanarwar ta kuma yi addu’ar All.. ya jikansa ya bai wa iyalansa hakurin jure rashi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!