Connect with us

Addini

Buhari ya jinjinawa sojojin da ke yaki da boko haram

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa dakarun operation lafiya dole da ke aikin samar da tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar nan.

 

Muhammadu Buhari wanda ministan tsaro manjo janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya ya wakilta, ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai shalkwatar dakarun operation lafiya dole da ke garin Maiduguri a jihar Borno.

 

Muhammadu Buhari ya kuma ce, ba ko shakka dakarun na operation lafiya dole suna iya kokarinsu wajen ganin sun kakkabe ‘yan ta’addar boko haram a fadin kasar nan.

 

Inda ya shaidawa sojojin da suka jikkata a bakin daga da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu da cewa, gwamnati za ta ci gaba da kula da halin da suke ciki don rage musu radadin halin da suka shiga sakamakon sadaukar da rayukansu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar NAJERIYA.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!