Connect with us

Kaduna

Tsaro: An kama ‘yan fashi da makami a Kaduna

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutane 15 da a ke zargin yan fashi da makami ne.

Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ASP Muhammad Jalige.

Jalige ya ce, wasu makiyaya ne suka kai wa rundunar yan sanda labarin ‘yan fashin, inda kuma suka yiwa maboyar ta su dirar mikiya.

A yayin kamen nasu ‘yan sanda sun samu nasarar kwato shanu sama da Hamsin.

A cewar rundunar ‘yan sandan za ta dauki matakin da ya dace a kansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!