Labarai
Buhari ya kara sama da Naira Biliyan 600 a aikin titin Kano zuwa Abuja
Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) a jiya laraba ta amince da sake fasalta aikin titin Kano zuwa Abuja.
Majalisar ta ce a yanzu za a kashe Naira Biliyan dari bakwai da casa’in da bakwai da miliyan dari biyu ne wajen gudanar da aikin.
Wannan dai na nuna cewa an samu karin Naira Biliyan dari shida da arba’in da biyu da miliyan dari biyu akan yadda aka tsara za a gudanar da aikin tun farko, a baya dai an tsara za a gudanar da aikin ne akan Naira Biliyan dari da hamsin da biyar.
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya laraba jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta kasa.
A cewar ministan tun farko an tsara aikin kwaskwariman titin ne akan kudi naira biliyan dari da hamsin da biyar ga kamfanin Julius Berger.
You must be logged in to post a comment Login