Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Buhari ya nada Amokachi a matsayin mai taimaka masa kan harkokin wasanni

Published

on

Daga Abdullahi Isa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon dan wasan Kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Daniel Amokachi a matsayin mai taimaka masa kan harkokin wasanni.
Hakan na cikin wata takardar shaidar nadin da Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta bai wa Amokachi a yau Alhamis.

Amokachi dai yana cikin tawagar yan wasan kasar nan da suka lashe kofin Afurka a shekarar 1994 a kasar Tunisia.

Haka zalika ya Kuma taka rawar gani a gasar cin kofin Duniya da kasar nan ta fara halarta wanda akayi a kasar Amurka a shekarar ta 1994.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!