Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wasan share fagen gasar cin kofin Afurka : Super Eagles za ta fafata da Saliyo

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles za ta yi wasanta na gaba na neman tiketin halartar gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2021,  a watan Nuwamba mai zuwa.

Najeriya dai za ta fafata da kasar Saliyo ne gida da waje a ranar tara ga watan Nuwamba da kuma ranar goma sha bakwai ga wata.

An dai cimma wannan matsaya ne ta zabar ranakun da za a ci gaba da gudanar da wasannin bayan wata tattaunawar gaggawa da hukumar kwallon kafa ta Afrika (CAF, ta gudanar a jiya Laraba, 19 ga watan Agusta.

Haka zalika, hukumar ta CAF ta kuma amince da tsayar da ranakun fitar da rukunin kungiyoyin dake neman tiketin halartar gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 wanda za a yi a kasar Qatar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!