Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya nemi afuwar ‘yan Najeriya kan sabunta rajistar ajiya na banki

Published

on

Gwamnatin tarayya ta nemi afuwar ‘yan Najeriya game da wani rahoto da ta fitar a jiya da ke cewa, kowane dan kasar nan da ke da asusun ajiya na banki da ya je ya sabunta rajistar asusunsa.

Dazu-dazun nan ne gwamnati ta fitar da sabon sanarwar tana mai cewa, an samu kuskure ne wajen fitar da waccan sanarwa domin kuwa lamarin bai shafi kowa da kowa ba.

Saboda haka hukumar tattara kudaden shiga ta kasa FIRS za ta fayyacewa al’ummar kasa yadda lamarin ya ke daga bisani.

Tun farko dai a jiya alhamis ne gwamnatin tarayya ta bukaci dukkannin masu asusun ajiya na bankuna ko cibiyoyin kudi a kasar nan da su gaggauta zuwa su sabunta rajistar asusun nasu.

Gwamnatin ta wallafa hakan ta cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a jiya alhamis.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!