Connect with us

Labarai

Buhari ya nemi sahalewar majalisar wakilai kan karin kasafin kudi

Published

on

Gwamnatin tarayya ta aikewa da majalisar wakilai karin kasafin kudi da za a kashe wajen samar da allurar rigakafin COVID-19 ga al’ummar kasar nan.

Ministar Kudi Kasafi da Tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a yau Alhamis, ta na mai cewa za a shirya daftarin kasafin kudin a watan Maris mai kamawa.

Ahmed tayi magana ne a jawabin farko na sanarwa da aka gabatar a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

“Karin kasafin kudi, na farko zai kasance a watan Maris game da annobar COVID-19 amma kuma za mu yi bitar tsakiyar shekara kamar yadda muka yi a bara na kasafin kudin.”

“Idan a lokacin muna yin bitar kuma akwai bukatar komawa don yin duk wani gyara na karin kasafin kudi, a wancan lokacin, za mu dauki wannan shawarar; idan ba haka ba, za mu kawo rahoton bita kawai,” inji ta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives