Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu baza jami’an mu don taya tsaftar muhalli – FRSC

Published

on

Hukumar kiyaye abkuwar haddura ta kasa FRSC ta ce za ta baza jami’anta a ranakun tsaftar muhalli don yaki da masu karya doka.

Babban kwamandan hukumar anan Kano Zubairu Mato ne ya bayyana hakan lokacin da yake karbar tawagar tsaftar muhalli na karshen wata.

Ya ce, suna sane da yadda wasu mutanen ke karya dokar tsaftar muhalli ta hanyar ci gaba da zirga-zirgarsu ta yau da kullum akan titina a don haka hukumar zata shiga cikin lamarin.

Zubairu Mato Wanda ya samu wakilcin shugaban sashin kula da tsaftar hukumar da da’ar ma’aikata Ali Ahmad Umar.

A ziyarar tsaftar muhalli ta wannan rana, kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya yabawa hukumar ta FRSC bisa yadda suka tsaftace ciki da wajen ta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!