Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje ya gargadi al’ummar Kano kan kiyaye dokokin tsaftar muhalli

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci al’umma jihar da su kiyaye karya dokokin da ta ke sanyawa a karshen kowanne wata da ake gudanar da tsaftar muhalli.

Kwamishinan muhalli na jihar Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun ma’aikatar Abbas Habeeb Abbas ya sanyawa hannu.

A cewar sanarwar tana gargadin iyaye da su killace yaran su domin kuwa hukuma za ta dau mataki kan yaan da ke gudanar da wasanni akan titina lokacin da ake tsaka da tsaftar muhalli.

Kazalika ta cikin sanarwar ta gargadi matuka baburan adaidaita sahu da su guji gudanar da ayyukan su a lokacin tsaftar muhalli, domin kuwa kotun tafi da gidan ka za ta yanke musu hukunci nan take.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!