Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya rabawa manoma irin shuka a Kano

Published

on

Mataimakin gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bukaci malaman Gona da kwararru kan aikin Noma, su rinka wayar da kan kananan manoma kan yadda za su shuka amfanin gonar su a wannan lokacin da aka fara samun zubar ruwan sama.

Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana hakan ne yayin da yake kaddamar da bayar da irin shuka kyauta ga kananan manoma da suka fito daga kananan hukumomi goma sha uku a nan jihar Kano, wanda cibiyar  wayar da kan manoma kan yadda za su yi shuka ta Gwamnatin tarayya wato ICRISAT ta kaddamar a yau Lahadi.

Ya kuma ja hankalin manoman da suyi amfana da tallafin irin shukar da suka karba ta hanyar data dace musamman, wajen shukawa a gonakin su don samar da albarkatun gona yadda ya kamata.

Da yake jawabi yayin bayar da tallafin shugaban cibiyar ta ICRISAT, Dakta Hakeem Ajeigbe cewa yai sun bayar da tallafin ne don taimakawa kananan manoma a wanannan lokacin da ake fama da halin babu sanadiyyar bullar cutar Covid-19, wanda ya sanya da yawa daga cikin manoman suka cinye amfanin gonar su.

Manoman jihar Kano sun mayar wa da CBN amfanin gona

Majalisa za ta binciki badakalar baiwa manoma rancen kudi

Wasu daga cikin manoman da suka amfana da irin shukar sun bayyana jin dadin su bisa tallafin da cibiyar ta ICRISAT ta basu, harma sukai kira ga gwamnatin Kano data samar musu da takin shuka a damunar bana don samun ribar abin da zasu shuga yadda ya kamata.

Kananan hukumomin da suka samu tallafin irin shukar sun hadar da karamar hukumar Bebeji da Minjibir da Garun Mallam da Rano da Bunkure da Dawakin Kudu da Bagwai da Bichi da Danbatta da Gezawa da Gabasawa da Tudin Wada sai kuma Gwarzo.

Akallam manoma dubu biyu ne zasu amfana da irin shukar da suka fito daga kanan hukumomi goma sha uku da irin shuka da ya hadar da na Dawa da Gero da Shinkafa da Wake.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!