Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Da dumi-dumi: Corona ta sake bulla a Sokoto

Published

on

Gwammatin jihar Sokoto ta sanar da sake bullar cutar Covid-19 a jihar.

Kwamitin karta-kwana kan yaki da cutar Corona na jihar ta Sokoto ya sanar a shafinsa na Twitter cewa ya karbi Almajirai 33 daga garin Zariya na jihar Kaduna a ranar 4 ga wannan watan da muke ciki na Yuni.

Sai dai a cewar kwamitin tun bayan da aka dawo da da su an killace dukkkan almajaran su 33 a san-sanin horar da masu yi wa kasa hidima dake Wamakko, yayin da aka cigaba da yi musu gwaji.

Amma abun takaicin shi ne 11 daga cikin 33 na dauke da cutar C0VID-19.

Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar kan su kwantar da hankalin su, su kuma cigaba da biyayya ga matakan da masana kiwon lafiya suka sanya domin dakile yaduwar cutar.

Har ila ya, sanarwar ta kara da cewar gwamantin jihar zata hada hannu da gwamnatin jihar Kaduna domin tabbatar da an killace makarantar ko tsangayar da almajiran ke karatu dake Zariya.

Kafin wannan sanarwa dai, a ranar Alhamis din da ta gabata gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da cewar daukacin masu dauke da cutar Corona a jihar sun warke.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!