Connect with us

Labarai

Buhari ya rage farashin man fetur

Published

on

Gwamnatin tarayya ta sanar da rage farashin man Fetur daga naira 145 zuwa naira 125, biyo-bayan karyewar farashin man a kasuwar duniya a dalilin bullar kwayar cutar Corona.

Kamfanin mai na kasa NNPC ne ya sanar da hakan a shafinsa na twitter, inda ya umarci gidajen man da su fara sayarwa a kan wannan farashi na naira 125 daga gobe alhamis.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da zaftare farashin bayan da karamin ministan man Fetur din kasar nan Timipre Sylva ya gabatarwa majalisar zartarwa ta tarayya rahoto a kai.

Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa Mr Timipre Sylva ne ya bukaci a rage farashin, a dalilin faduwar farashin na sa a kasuwar duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!