Labarai
Gwamnatin Kano ba ta tallafawa kasuwar Rimi -Shugaban kasuwar
Shugaban Kasuwar Rimi dake nan Kano Alhaji Salisu Ya’u Yola ya ce babu wani aikin ci gaba da kasuwar ke samu daga bangaren gwamnatin jihar Kano da karamar hukumar birni a halin yanzu.
Shugaban kasuwar Alhaji Salisu Ya’u Yola ne ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce akwai tarin matsaloli dake addabar al’ummar kasuwar da suka hada da matsalar tsaro sakamakon rashin samar da haske a cikin kasuwar da gefanta.
Akwai bukatar samar da kasuwar mata zalla a Kano
Waiwaye: Shekaru 14 cif da kisan Hajiya Sa’adatu Rimi
KAROTA tayi wawan kamu a kasuwar Singa
Shugaban kasuwar ya kara da cewa rashin samun cikakken goyon baya daga gwamnati shi ya sanya kasuwar ke samun koma baya ta fannin tattalin arziki.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito Salisu Ya’u Yola na kira ga gwamnatocin biyu da su kawo wa kasuwar Rimi dauki kasancewar kasuwa ce mai tsohon tarihi.
You must be logged in to post a comment Login