Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya sauka ko majalisa ta tsige shi – Kungiyoyin fafaren hula 44

Published

on

Wasu gamayyar kungiyoyin farar hula 44, sun roki Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauka daga kujerara sa ko kuma Majalisar Dokoki ta tsige shi idan har ba zai iya tabbatar da tsaro da walwalar mutanen Najeriya ba.

Kungiyoyin sun gabatar da wannan bukatar ne a wani taron gaggawa na gamayyar kungiyoyin fararen hula da suka yi game da halin da kasar ke ciki a Abuja.

Kazalika kungiyoyin sun tuhumi shugaba Buhari da ya kawo karshen rashin hukunci, a cewarsu Najeriya ta zama kundin tsarin zubar da jini a karkashin jagorancin Shugaba Buhari.

Kungiyoyin sun koka kan yadda gwamnatin tarayya ta gaza sauke nauyin da ke kanta na tsaro, musamman ma kalaman da Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi mai ritaya yayi a baya bayan nan, wanda ya kira ‘yan Najeriya da cewa matsorata ne tare da bukatar ‘yan Najeriyar su kare kansu daga ‘yan fashi da sauran masu laifi.

Sun jaddada cewa irin wannan bayanin na iya kawo cikas ga yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya da ‘yan ta’adda.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!