Connect with us

Labarai

Za mu kawo karshen siyasar jagaliya a Kano – Kwamishinan ‘yan sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce za ta yiwa siyasar jihar Kano garanbawul domin magance rikice rikicen ‘yan jagaliyar siyasa na sare sare.

 

Kwamishin ‘yan sandan Kano Samaila Shuaibu ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai

 

Samaila Shuaibu ya ce hakan ba zai samu ba har sai an samu hadin kan malaman addinai da sauran masu rike da masarautun gargajiya har ma da gwamnatin Kano don tabbatar da tsaro a jihar baki daya.

 

Samaila Shuaibu ya ce, matukar ‘yan jaridu da sauran kungiyoyin kare hakkin al’umma da na matasa yan kishin kasa suka bada hadin kai ga rundunar ‘yan sandan shakka babu za’a samu raguwar aikata muggan laifuka a Kano.

 

Samaila Shuaibu ya kuma ce za a tabbatar da tsaro ga duk wanda ya kai wa rundunar bayanan sirri don bankado maboyar batagari da sauran guraren masu aikata laifuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!