Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Buhari ya shirya yakar Corona a Kano

Published

on

Gwamanatin tarayya ta ce a shirye take da ta tallafawa jihar Kano da dukkan abinda take bukata domin yakar cutar Corona.

Shugaban tawagar masana daga fadar shugaban kasa da suka zo Kano yau Talata Dakta Nasir Sani Gwarzo ne ya bayyana hakan lokacin da suka kawo ziyara fadar Gwamnatin Kano.

Ya kara da cewa makasudin zuwan su Kano shi ne domin su isar da sakon shugaban kasa dana ministan lafiya dongane da Cutar Corona.

Yace adon hakane aka bukace su dasu tuntubi abinda ake bukata na tallafi tare da tsayawa ayi komai dasu.

Da yake jawabi gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin ziyarar tasu  jinjinawa shugaban kasa ya yi tare da tabbatar da cewa za su basu dukkan goyon bayan da ya kamata a aikin na su.

Gwamnan na Kano ya ce daga cikin abinda gwamnatin Kano ke bukata akwai karin wasu cibiyoyin gwajin cutar ta Corona a jihar ta Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!