Connect with us

Coronavirus

Covid-19: Tawagar gwamnatin tarayya da za ta tallafawa jihar Kano ta iso

Published

on

Rahotanni na bayyana cewa tuni tawagar shugaban kasa kan yaki da Coronavirus ta iso fadar gwamnatin Kano karkashin jagorancin Dr.Nasir Sani Gwarzo.

Dr. Nasir Sani Gwarzo yace tawagar ta iso nan jihar Kano ne don bada gudunmawar da ta dace ta bangaren gwamnatin tarayya, a yakin da ake yi da cutar Covid-19 a jihar Kano.

Wakiliyar mu ta fadar Gwamnatin Kano Zahra’u Nasir ta ruwaito Dr. Sani na cewa tawagar zata yi aiki da kwamitin yaki da cutar da ke nan Kano, yana mai cewa suna fatan samun dukannin goyon bayan da ya dace daga gare su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!