Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya tuhumi jami’an tsaro kan ‘yan ta’adda

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tuhumi hafsoshin tsaron kasar nan kan hanyoyin da ‘yan bindiga a arewa maso gabashin kasar nan ke bi wajen samun makamai duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin kasar nan.

Haka kuma shugaban kasa Buhari ya yi watsi da batun da ake yadawa cewa ‘yan ta’adda a kasar nan na da kudade da kayayyakin aikin da suka fi na jami’an tsaro a kasar nan.

Shugaba Buhari dai ya yi wadannn bayanai ne a yayin taron kungiyar gwamnoni, inda suka bukace shi da ya basu wasu ‘yan kudaden tallafi la’akari da yadda suke kashe kudade wajen taimakawa jami’an tsaro a jihohin su.

Shugaba Buhari ya kuma bukace gwamnonin da su tsaya tsayin daka wajen kare al’ummomin su, tare kuma da hada kai wajen raba bayanann sirri tsakanin dukkanin jami’an tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!