Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

PENGASSAN : Sun tsunduma yajin aikin gargadi

Published

on

Wasu ma’aikata da ke cikin uwar kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar Gas ta kasa “PENGASSAN’ wadanda suke aiki a ma’aikatar man fetur ta kasa da sauran hukumomi da ke karkashinta sun tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki uku.

Rahotanni sun bayyana cewa, tun da fari wasu manyan ma’aikatan kungiyar sun gudanar da zanga-zanga don nuna adawa da sanyasu cikin tsarin biyan albashi na IPPIS.

Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar Fortune Obi ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa, a yayin zanga-zangar da manyan ma’aikatan kungiyar suka gudanar dauke da takardu masu bayyana cewa tsarin biyan albashi na IPPIS ya fi annobar covid-19 illa a don haka akwai bukatar shugaban kasa ya dauki mataki tare da girmamma alkawuran da ya daukarwa kungiyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!