Connect with us

Labarai

Buhari ya umarci jagororin tsaro da su zakulo ‘yan ta’adda da masu daukar nauyinsu.

Published

on

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro manjo janar Babagana Monguno mai ritaya, ya ce,  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jagororin tsaron kasar nan da su yi duk me yiwuwa wajen ganin sun zakulo ‘yan ta’adda da masu daukar nauyinsu a duk inda suke a fadin kasar nan.

A cewar shugaban kasar wajibi ne a hukunta duk wadanda suke daukar nauyin tashe-tashen hankula a Najeriya.

A yayin zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a yau talata manjo janar Babagana Monguno mai ritaya ya ce shugaba Buhari ya ba da wannan umarni ne yayin taron da ya gudanar da jagororin tsaron a fadar asorok.

Janar Babagana Monguno ya ruwaito shugaban kasar na cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci ci gaba da zubar da jinin jama’a babu gaira babu dalili ba da ke ci gaba da faruwa a kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!