Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya yi tir da harin da aka kai wa ma’aikatan bada agaji a Borno

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi All…..wadai da kisan da ‘yan bindiga suka yiwa wasu ma’aikatan bada agaji a jihar Borno tare da yin garkuwa da wasu guda biyu.

Awatan da ya gabata ne dai ‘yan bindigar su ka yi garkuwa da mutanen.

Hakan na cikin wata sanarwa ce da babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar a jiya Laraba.

Sanarwar na dauke da sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan guda biyar da ‘yan tada kayar bayar suka kashe a baya baya nan.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin tarayya za ta yi duk me yiwuwa wajen kawo karshen ayyukan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar nan.

Sai dai sanarwar ta kuma jinjinawa jami’an tsaron kasar nan da irin sadaukarwar da suke wajen ganin sun dakile ayyukan boko Haram da sauran ta’addanci.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!