Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

‘Yan sanda sun kama masu aikata laifuka a Kaduna

Published

on

Rundunar ‘yan-sandan Jihar Kaduna ta ce, ta kama wadanda ta ke zargin aikata laifuka daban-daban ciki har da masu yin garkuwa da mutane da masu satar Shanu da masu ta da zaune tsaye dari biyu da goma sha Bakwai.

Kwamishina ‘yan sandan na jihar Malam Umar Muri ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai.

A cewar kwamishinan Umar Muri suna zargin wadancan mutanen ne da aikta manyan laifuka tsakanin watan Afrilun zuwa watan Yuli bana.

A cewar sa, sun kuma kwace muggan makamai har Arba’in da uku wadanda tuni ya bada umarnin kai su inda ba wanda zai gansu kafin rundunar ta yanke hukunci akan su.

Kwamshinan ya kira ga la’umma da su ci gaba ba su hadin kai don kawo karshen ta’andanci a fadin kasar nan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!