Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Corona : Jihar Niger zata bude makarantu a mako mai zuwa

Published

on

Gwamnatin jihar Niger za ta bude makarantun jihar a ranar hudu ga watan gobe na Oktoba domin kammala zangon karatu na uku na wannan shekara ta 2020.

Kwamishiniyar Ilimi ta jihar Hajiya Hannatu Salihu ce ta bayyana hakan yayin zantawa da masu ruwa da tsaki kan batun komawar dalibai makaranta a jihar.

Ta kuma umarci malaman makarantun jihar da su fara shirye-shiryen komawa makaranta daga yau Talata 29 ga watan Satumbar da muke ciki.

Hajiya Hannatu Salihu ta ce daliban karamar sakandire za su rika zuwa makaranta da safe yayin da daliban babbar sakandire za su rika zuwa da yamma.

Sai dai ta jaddada cewa dukkanin daliban za su fara zuwa makarantar ce cikin bin dokokin kare kai daga kamuwa da cutar corona don takaita yaduwarta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!