Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari zai samar da guraben ayyuka miliyan biyar

Published

on

Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya kara jaddada matsayar gwamnatin tarayya na kirkiro da guraben ayyuka akalla miliyan biyar ga al’ummar kasar nan

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin wani taro da cibiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta jihar Lagos ta shirya wanda aka gudanar ta kafar Internet.

Ya ce, gwamnati tana kokarin bunkasa bangaren aikin noma da samar da gidaje masu rahusa da bunkasa masana’antu wanda hakan za su taimaka gaya wajen samar da ayyukan yi ga miliyoyin ‘yan Najeriya.

 

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa, gwamnati za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga masu sha’awar zuba jari daga ketare dana cikin gida don rage rashin ayyuka tsakanin matasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!