Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari zai tafi Habasha don bikin rantsar da Firaministan ƙasar

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin zai tashi zuwa birnin Addis Ababa don halartar bikin rantsar da Firaministan Habasha Abiy Ahmed.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa Femi Adesina ya fitar a ranar Asabar a Abuja.

A cewar Adesina, shugaban zai bar Abuja zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha, ranar Lahadi.

Za a gudanar da bikin rantsar da firaministan Habasha Abiy Ahmad a wa’adin mulkin sa karo na biyu tsawon shekaru biyar.

Hadimin shugaban ƙasar ya bayyana cewa shugaba Buhari zai isar da sakon fatan alheri a bikin rantsar da Abiy Ahmad.

Sanarwar ta rawaito cewa shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin Waje Geoffrey Onyeama, da darakta janar na hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i.

Ana sa ran shugaba Buhari zai dawo Abuja ranar Talata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!