Labarai
Buharii ya amince da kashe Biliyan 600 don gyaran matatar mai ta Fatakwal.
Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) ta amince da ware dala biliyan daya da rabi kwatan-kwacin naira biliyan dari shida don gudanar da aikin gyara matatar mai ta garin Fatakwal da ke jihar Cross River.
An dau wannan mataki ne yayin taron mako-mako da majalisar zartarwa ta kasa ta gudanar a yau wanda shugaba Buhari ya jagoranta.
Karamin ministan man fetur Timipre Sylva ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labaran fadar shugaban kasa bayan kammala taron.
‘‘Ma’aikatar man fetur ta mika da bukatar aikin gyaran matatar mai ta garin Fatakwal akan kudi dala biliyan daya da miliyan dari biyar, wanda kuma mambobin majalisar ta zartarwa suka amince’’
‘‘Saboda haka muna farin cikin sanar da ‘yan Najeriya cewa, nan ba da jimawa ba, za a fara aikin garambawul ga matatar man, kuma za a kasafta aikin ne gida uku, za kuma a dauki tsawon watanni goma sha takwas kafin a kammala’’ inji Timipre Sylva.
You must be logged in to post a comment Login