Addini
Bukukuwan Mauludi sun kankama a Kano
Al’ummar musulmi daga ko ina a faɗin duniya na ci gaba da gabatar da bukukuwan mauludi domin murnar zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta manzon tsira Annabi (s.a.w) wanda ake yi duk shekara a wannan wata na Rabi’ul Auwal.
Malam Ibrahim Ɗan Liti na cikin masu shirya taron mauludi a makarantar babban malami na Madabo da ke nan Kano, ya shaida wa wakilinmu Abdurrahman Hamisu Namadina cewa su kan yi shirye-shirye na musamman tare da gayyatar al’ummar musulmi duk shekara domin karantar da tarihin manzon rahma.
Tun kafin shigowar wannan wata dai al’umma kama daga yara da manya, da maza da mata suka fara shirya tarukan mauludin a sassan Kano.
Ana kawata wuraren Mauludi
Musulmi kan ƙawata wurin mauludi da ado kala-kala masu ɗaukar hankali domin girmamawa ga Manzon tsira (s.a.w).
Me ake yi a wurin Mauludi?
Jigon abubuwan da ake yi a wurin bikin shi ne karantar da tarihin Manzo, da kuma koyar da ibadu bisa tsari da tarbiyyar addinin Islama.
Haka kuma a kan rera ƙasidun bege sannan a na bai wa ɗalibai karatu wanda su kan haddace su kuma gabatar a ranar mauludin.
Wasu mahalarta Maludi sun shaidawa Freedom Radio cewa, suna shiga cikin farin ciki mara musaltuwa a duk sandan watan yazo, domin murna da ranar haihuwar Annabi Muhammad (s.a.w).
Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi
Limamin jumu’a a Kano yayi Allah-wadai da “Black Friday”
Sheikh Mustaphal Bukhari Sheikh Yusuf Makwarari malamin addinin musulunci ne wanda ke gabatar da wa’azi a wuraren Mauludi, da yake zantawa da Freedom Radio ya yi kira ga matasa kan su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun halarci wuraren mauludi domin dai samun dacewa.
Ana bikin Mauludi ba dare ba rana a Kano
Al’ummar musulmai dai kan shafe tsawon wannan wata dama wani ɓangare na wata mai biye masa cikin gudanar da bukukuwan na mauludi.
A nan Kano ma, duk inda ka zaga ba dare ba rana zaka iske wurare da dama na gabatar da tarukan mauludin.
Tarihin musulunci dai ya nuna cewa, ranar 12 ga wannan wata da mu ke ciki na Rabi’ul Auwal ita ce ta zo daidai da ranar haihuwar manzo (s.a.w).
You must be logged in to post a comment Login