Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Adabin Hausa

Burin mu samar wa da matasa sana’o’i ta hanyar fasaha-British Council

Published

on

Cibiyar yaɗa al’adun gargajiya na ƙasar Birtaniya , British Council ta tabbatar da cewar zata cigaba da yin duk mai yiwuwa ta hanyar haɗaka da kuma tallafawa don ganin an samu matasa da zasu dogara da kansu ta hanyar fasaha da ƙirƙire na zane.

Babban jami’in ƙungiyar Start Up Kano, kana jami’in hadin gwiwar gudanar da shirin ƙirƙirar fasaha da tattalin arziki , na cibiyar ta British Council a Kano, Umar Muhammad ne ya bayyana haka , a wani shirin bajakolin fasahar ƙirƙire-ƙirƙire da zane da ya gudana a Kano.

Umar, wanda ya kasance shugaban gudanar da shirin a Madadin British Council, yace tsarin an yi shi ne domin fito da fasahar matasa da kuma samar musu hanyar madogara mai ɗorewa da zasu samu sana’o’in dogaro da kai.

“Wannan shirin an yi shi ne musamman don ganin an samar da hazikan matasa, a gefe ɗaya kuma an zaburar dasu don su cigaba da bayyana fasahar da Allah yayi musu ta hanyar yin zane da ƙirƙira”

“Kowa da yadda rayuwa take kasance masa kuma kowa da irin baiwar sa, don haka aka tsara bikin da niyyar ɗora su a tafarkin da zasu dogara da kansu ta hanyar baiwar su ” inji Umar Muhammad.

Ana ta ɓangaren wacce ta kafa Makarantar Zane da fasaha ta Pint Box Academy , kuma daya daga cikin wanda suka gudanar da taron tare da British Council, Jamila Nuhu Batagarawa, ta ce lokaci yayi da za a kawo karshen koma baya da jihar Kano da kuma Arewacin ƙasar nan ke samu a ɓangaren ƙirkire ƙirƙire da fasaha.

Tarin matasa Maza da Mata ne a Kano suka baje kolin fasahar su na ƙirƙira, Zane, gine -gine da makamantansu, da ƙungiyoyin Fasaha suka jagoranta a jihohin Kano , Lagos sai birnin tarayya Abuja da kuma Port Harcourt.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!