Connect with us

Kiwon Lafiya

Burtaniya ta gamsu da sakamakon zabukan shugaban kasa da ‘yan majalisu

Published

on

Burtaniya ta ce ta gamsu da sakamakon zabukan shugaban kasa dana ‘yan majalisun dokokin tarayya da aka gudanar a kasar nan a ranar Asabar da ta gabata.

Minista mai kula da nahiyar Afirka Harriett Baldwin ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba.

A cewar sanarwar, zaben da sakamakon sa an yi sune akan idanun masu sanya idanu na cikin gida da a ketare, wanda kuma dukkanninsu sun yaba da sakamakon sa.

Harriett Baldwin a cikin sanarwar ya kuma taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari Murnar sake darewa karagar mulki karo na biyu.

Haka kuma sanarwar ta kuma ce al’ummar Nigeriya sun nuna irin bajinta da kuma wayewa da suke da shi a bangaren dimukuradiya ,a don haka ta bukaci hukumar zabe ta kasa INEC da ta yi gyara a dan bangarorin da aka samu matsaloli a yayin zaben na makon jiya a zabukan da za a yi anan gaba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!