Labaran Wasanni
AFCON 2022: Kasar Senegal ta kai wasan karshe
Kasar Senegal ta kai zuwa wasan karshe na gasar cin kofin Afrika da ake gudanarwa a kasar Kamaru.
Senegal dai ta samu nasara kan kasar Burkina faso da ci 3-1 wanda hakan yasa ta samu tikitin zuwa wasan na karshe.
An buga wasan dai a ranar 2 ga watan Fabrairu 2022.
Dan wasan kasar Senegal Diallo ne ya fara zura kwallo a ragar Burkina Faso a mintuna na 69 daya samu taimako ta hannun Kalidu Koulibaly sai kuma dan wasa Gueye ya kara a mintuna na 75 bayan samun taimako daga hannun Sadio Mane a mintuna na 81 dan wasan Burkina Faso Taure ya cirowa kasar sa kwallo daya inda kuma a mintuna na 86 Sadio Mane ya karawa kasar sa ta Senegal Kwallo.
Yanzu dai kasar Senegal za ta buga wasan karshe ne tsakanin kasar Eghpt ko kuma kasar Camaroon da za su buga wasa a gobe Alhamis 03 ga watan Fabrairun 2022.
You must be logged in to post a comment Login