Rahotonni
Canjin yanayi na haifar da kwararowar hamada – Masani
Wani masanin tsirrai da aikin noma ya bayyana canjin yanayi da cewa daya ne daga abubuwan da ke haifar da kwararowar hamada da fari musamman a kasashe masu zafi.
Kamaludden Tijjani Aliyu na cibiyar Samar da amfanin gona na kasashe masu zafi wato IITA ne ya bayyana hakan a yayin zantawa da Freedom Radio a wani bangare na ranar yaki da kwararowar hamada da annobar fari ta duniya da ake gudanarwa a yau.
Ya ce, kaso 24 na kwararowar hamada da fari na samo asali da yadda manoma ke yin huda a yayin ayyukan noma, Wanda hakan ke ragewa kasa tasiri.
Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso yace, gwamnati zata fara kaddamar da hukuncin doka ga masu sare bishiyu da zarar ta samu sahalewa daga majalisar dokokin jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login