Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Caf Champions League: Rivers United za ta kara da Al-Hilal

Published

on

Wakilan Najeriya a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafar Afrika ta Caf Champions League Rivers United, za ta kara da Sudanese Al-Hilal a zagaye na gaba.

Rivers United dai ta doke Young Africans da ci 1-0 a ranar Lahadi 19 ga watan Satumbar shekarar 2021.

NPL: Kano Pillars ta yiwa ‘yan wasa 32 rijista

Hakan yasa kungiyar ta Rivers United ta samu nasara kan Young African din a wasan gida dana waje da kuma jumullar kwallaye 2-0.

Ita kuwa kungiyar Al-Hila ta samu nasarar kaiwa mataki na gaba bayan kunnan doki 1-1 da ta yi da tawagar kasar Ethiopia Fasil Kenema.

Wasan farko tsakanin kungiyoyin a birnin Addis Ababa na kasar ta Ethiopia an tashi 2-2 wanda hakan ya bawa kungiyar Al-Hilal damar zuwa mataki na gaba.

Wasan dai za’a gudanar dashi a ranar 14 ga watan Oktoba na shekarar 2021.

Rivers United ce za ta karbi bakuncin zagayen wasan na farko.

Yayin da a ranar 21 ga watan na Oktoba a buga wasa zagaye na 2 a birnin Omdurman dake kasar ta Sudan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!