Connect with us

Labaran Wasanni

Tsohon dan wasan Tottenham Hotspurs Jimmy Greaves ya mutu

Published

on

Tsohon dan wasan kasar Ingila da Tottenham Hotspurs , Jimmy Greaves ya mutu yana da shekaru 81.

Tawagar dan wasan ta Tottenham ce ta bayyana haka a shafinta na Internet, inda ta ce dan wasan ya mutu ne a gidan sa.

Greaves , ya zura kwallaye 266 a wasanni 379, da ya wakilci kungiyar ta Tottenham daga shekarar 1961 zuwa 170, da har yanzu shi ke kan gaba ba tare da an kamo yawan kwallayen sa.

Greaves ya dauki gasar Kofin Duniya na shekarar 1966, inda ya wakilci Ingila sau 57 tare da zura kwallaye 44, inda dan wasa Gary Lineker da Kwallo 48 sai Bobby Charlton da 49 da Wayne Rooney da 53 ne ke a gaba da shi da yawan kwallaye.

“Muna Mika sakon ta’aziyyar mu ga matar sa Irene da yaran sa 04 da jikokin sa 10 da yaran jikokin sa ” a sanarwar da kungiyar Tottenham ta wallafa a shafinta na Internet.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!