Coronavirus
CBN ya ceto kasar nan daga yunwa ana tsaka da COVID -19 – Godwin Emefiele
Babban bankin kasa CBN ya ce, ya ceto kasar nan daga karancin abinci da barazanar fadawa yunwa a yayin da ake tsaka da fama da annobar Covid-19.
Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na bankin Isaac Okorafor ya fitar, inda ya ce babban bankin kasa ya musanta batun kwamitin tattalin arziki da ya ce bankin ya gaza wajen tabbatar da ingancin shirye-shiryen samar da abinci da fitar da jama’ar kasar nan daga matsanancin talauci.
A ranar litinin din da ta gabata ne kwamitin tattalin arziki na kasa ya ce an sami wawakeken gibi a batun samar da abinci da kare al’ummar kasar nan daga fadawa halin yunwa, duk kuwa da makudan kudaden da babban bankin kasa CBN ya ware don yin hakan.
Sai dai ko da bankin ke mayar da martani kan zargin, ya ce yana iya bakin kokarin sa wajen ganin an yi amfani da kudaden da ya ware wajen samar da abinci da kuma rage radadin talauci.
Bankin bai tsaya iya nan ba, sai da ya bada misali kan yadda al’ummar kasar nan dubu 103 da dari 189 suka amfana da tsabar kudi naira biliyan 59 da miliyan 12 don rage musu radadi.
You must be logged in to post a comment Login