Connect with us

Labarai

CBN ya fitar da sabon tsari kan hurda da bankin da babu kudin ruwa

Published

on

Babban bankin kasa (CBN), ya fitar da sabon ka’ida ga masu gudanar da harkar banki da babu kudin ruwa a ciki.

Bankin na CBN ya bayyana cewa, wannan ka’ida da ya fitar yana cikin asusun tallafawa tsarin harkokin noma don riba da kanana da kuma matsakaitan sana’oi.

Bankin na CBN ya bayyana hakan ne ta cikin shafinsa na internet a ranar talata.

A cewar CBN, ka’idojin guda goma da ya fitar za su taimaka wajen bunkasa harkokin noma da kuma harkokin kanana da matsakaitan sana’oi.

Mai magana da yawun bankin na CBN Isaac Okorafor, ya ce tsarin zai yi matukar tasiri wajen farfado da komadar tattalin arzikin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!