Labarai
CBN ya sake gyara fasalin harajin shigo da kayayyaki
Babban bankin Nijeriya CBN, ya sake gyara fasalin farashin harajin shigo da kayayyaki ta iyakokin ruwa da na tudu, wanda harajin na hukumar hana Fasa Kwauri kudade ne da ake karba daga hannun masu shigo da kayayyakin waje kafin sahale shigo da kayan da sayar da su.
Ana biyan kudaden ne ta bankunan kasuwanci ga Hukumar Kwastam wadda ke karba a madadin gwamnatin tarayya.
Sabbin bayanai da aka buga a wata kafar kasuwancin gwamnatin tarayya sun nuna cewa masu shigo da kaya daga Najeriya za su siya dala akan Naira 1,457 da Sabon farashin ya nuna karin kashi 2.99% daga yadda ya gabata a baya na Naira 1,414 kan kowace dala tun daga ranar Juma’a 10 ga watan nan da muke ciki na Mayu.
A karkashin sabon umarnin babban bankin na CBN, hukumar kwastam za ta kididdige kudaden da za ta karba ne bisa la’akari da sauyin farashin musayar kudi da aka samu.
You must be logged in to post a comment Login